Fiye da fursunoni 40 na Isra’ila da ke hannun kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa ne suka mutu a hare-haren da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka yi ta kaddamarwa kan al’ummar yankin tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, kamar yadda wani rahoton baya-bayan nan na jaridar New York Times ya bayyana.
Binciken, wanda jaridar ta New York Times ta buga a wannan Asabar, ya ce fursunoni 41 daga cikin fursunoni 251 na Isra’ila da ake tsare da su a Gaza, an kashe su ne ta hanyar bama-bamai da Isra’ila ta yi ta jefawa kan yankin.
Binciken ya dogara ne akan rahotanni da kuma binciken soji kan mutuwar fursunonin, da hirarraki da sojoji da jami’an Isra’ila, da kuma wasu daga cikin dangin wadanda aka kama.
Jaridar ta yi nuni da dagewar da Netanyahu ya yi na ci gaba da yakin Gaza domin kubutar da wadanda ake tsare da su ta hanyar daukar matakan soji maimakon daukar matakin kawo karshen fadan ta hanyar tattaunawa da kuma musayar fursunoni, wanda kuma bayan kisan dubun-dubatar mutanen Gaza, da ma wasu daga cikin fursunonin Isra’ila, Netanyahu ya dawo ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni.