Sakatare-Janar na kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah ya yi jinjina ta musamman ga “jajirtattun mayaka a Gaza, wadanda ya bayyana su da manyan jarumai, da kuma sauran al’umma masu hakuri da juriya da ke Gaza, tare da bayyana su a matsayin abin koyi a wannan zamani na zalunci.
A yayin jawabinsa na tunawa da ranar ashura a jiya Laraba a birnin Beirut na kasar Lebanon, Sayyid Nasrallah ya jaddada cewa, ci gaba da gwagwarmaya na nuni da samun nasara ga daukacin al’ummar yankin da suka sha fama da wuce gona da iri daga haramtacciyar kasar Isra’ila, da mamaya, kisan kiyashi, da kuma wuce gona da iri. yana mai cewa, “darasin Ashura shi ne tsayawa tsayin daka tare da wadanda aka zalunta.
Sayyid Nasrallah ya bayyana cewa tallafin da kungiyar Hizbullah ke bayarwa ya shafi Falasdinu, da yankin Zirin Gaza da ake zalunta, da yammacin kogin Jordan, da kuma al’ummar kasar Labanon, inda ya kara da cewa, kasar Lebanon ta shiga wani sabon mataki tun ranar 8 ga watan Oktoba, tare da shiga sahun gaba wajen tunkarar zaluncin Isra’ila da take yi kan al’ummar Falastinu musammana Gaza.
Muna goyon bayan bangarorin kasashen Yaman da Iraki, Syria da Iran, wadanda suka hade a matsayin kawaye masu tsayin daka domin goyon bayan al’ummar Falastinu a dukkanin matakai.
Sayyed Nasrallah ya ci gaba da jaddada cewa, har yanzu akwai kasashen Larabawa uku da ke fama da mamayar Isra’ila, da wuce gona da iri, da ta’addanci: Falasdinu, Labanon, da Siriya.
Ya kuma yaba da goyon bayan da kasar Yamen ke baiwa zirin Gaza yana mai cewa: Kasar Yemen ta samu nasarar hana jiragen ruwa na Isra’ila da kuma masu taimaka mata, ratsawa ta cikin tekun Bahar Maliya zuwa Palastinu da Isra’ila ta mamaye, tare da kakaba wa tashar ruwan Eilat takunkumi, lamarin da ya jefa harkar zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci zuwa Isra’ila a cikin gagarumar matsala.