Shugaban kamfanonin Aliko Dangate ya bayyana cewa, ci gaban da kasashen Afirka suke na shigo da kayaki daga kasashen waje, yana kwacewa kasashen yankin ayyukan yi ne.
Jaridar Leadership ta Najeriya nakalto Aliko dangote yana fadar haka a hirar da ta hada shi da wakilin Jaridar ‘Finalcial Time Afrika’ David Pilling a taron FT Africa London a jiya Laraba.
Dangote ya kara da cewa dole gwamnatocin kasashen nahiyar su tallafawa kamfanoni na cikin gida don su tsaya da kafafuwansu su kuma samjar da ayyukan yi da mutanen yankin.
A wani bangare Dangote ya ce kamfanoninsa zasu kashe Biliyon $50 a zuba jari daga shekara ta 2026-2030 a nahiyar. Kuma ya sami damar sayan kasha 25% na kamfanin shimfida bututanmai a kasar Kenya tare da taimakon gwamnatin kasar.
Attajirin ya bayyana cewa shirinsa na rarraba man fetur a nahiyar Afirka yana tafiya kamar yanda ya tsara ya kuma kara da cewa tsarin rarraba man fetur a nahiyar zai hada da kasashen Djibuti, Habasah, Camaru da kuma Namibia.