Musulmi a jiya jumma’a a kasashen Yemen da Bahrain sun fito zanga zangar nuna goyon baya ga al-ummar Falasdinu da kuma yin allawadai da HKI da kuma masu goyon bayanta.
A kasar Yemen kamar yadda suka saba a ko wace Jumma’a miliyoyin mutanen kasar ne suke fitowa kan titunan birane da lardunan kasa don nuna goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu wadanda HKI da kawayenta sukewa kissan kare dangi a Gaza.
A birnin sannan babban birnin kasar miliyoyin mutane sun fito zuwa dandan 70 dake wajen birnin . Kuma kamar yadda aka saba malaman addini da kuma Jami’an gwamnatin kasar sun gabatar da jawabai wadanda suke nuna goyon bayansu ga Falasdinawa wadanda suke fafatawa da HKI a gaza.
A kasar Bahraini kuma dubban musulmi ne suka fito zanga zangar goyon bayan al-ummar falasdinu a gaza bayan sallar Jummma’a a unguwar al-Daraz dake birnin Manama babban birnin kasar.
Masu zanga zangar sun bukaci a bude hanyoyin shigar da kayakin agaji zuwa Gaza a kuma dakatar da yaki.
Daga karshe masu zanga zangar sun bukaci sarakunan Ali Khalifa su saki fursinonin siyasa a kasar wadanda suke kulle a cikin gidajen yarin kasar.