Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Idan yahudawan sahayoniyya suka hargitsa yankin Gabas ta Tsakiya, Iran a shirye take ta taka musu burki
Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri Kani ya yi nuni da cewa: Yahudawan sahayoniyya suna kokarin kawo rudani a wannan yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai jaddada cewa Iran ta kuduri aniyar yin amfani da karfinta wajen mayar da kakkausar martani ga wannan ‘yar ta’addar gwamnatin matukar ta kunna wutar tashe-tashen hankula a yankin.
A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta CNN ta Turkiyya: Baqiri Kani ya yi ishara da hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus na kasar Siriya, ya kuma ce: Wannan harin ya tilastawa Iran yin amfani da na’urorin tsaro masu muhimmanci yadda ya kamata da kuma hankali wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar yankin.
Ya ci gaba da cewa: Ya yi imani yahudawan sahayoniyya sun sani cewa, a yayin da yankin yake fuskantar barazana da rashin kwanciyar hankali da kuma matsalolin tsaro, tabbas Iran zata yi amfani da karfinta yadda ya kamata da kuma hikima wajen shawo kan duk wata matsala da daidaita al’amura. Baqiri ya yi kira ga kasashen musulmi da su yanke duk wata alaka da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai jaddada cewa: Sun yi imanin cewa, mataki mafi inganci da kasashen musulmi za su iya dauka shi ne kawo karshen duk wani hadin gwiwar siyasa da tattalin arziki da yahudawan sahayoniyya, domin mayar da ita saniyar ware a yankin.