Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Dole ne duniya ta dauki matakan kalubalantar muggan ayyukan ‘yan sahayoniyya
Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri ya jaddada cewa: Dole ne duniya ta hada karfi da karfe wajen kalubalantar muggan ayyukan wadanda ake kira gwamnatin yahudawan sahayoniyya wadanda suke haddasa rashin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, tare da daukar matakan keta dokokin kasa da kasa don taka musu burki daga munanan manufofinsu na nema kara kunna wutar tashe-tashen hankula da rikice-rikice a yankin.
A tattaunwarsa ta hanyar wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Hungary Peter Szijjártó, wanda kasarsa ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar turai, mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri a yammacin jiya Litinin ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya, tare da yin Allah wadai da matakin irin ayyukan da yahudawan sahayoniyya suke dauka wajen yin fatali da dokokin kasa da kasa da kuma halaltacciyar hakkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajen kare tsaronta da ikonta na kasa da kuma cikakken amincin kasarta.
A nashi bangaren, ministan harkokin wajen kasar Hungary Peter Szijjártó ya bayyana cerwa: A shirye kasarsa ta ke na ci gaba da tattaunawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai cewa: Muna matukar damuwa da abin da ke faruwa a kasar Lebanon da kuma ci gaba da tada zaune tsaye a yankin. Peter ya jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su yi duk abin da za su iya wajen dakile duk wani tashin hankali da rikici, domin ana iya daukar wadannan tashe-tashen hankula a matsayin barazana ga Turai.