Ministan Tsaron Kasar Iran Ya Gana Da Shugaba Bashsar Asad Na Syria

Ministan tsaron Iran  Azizi Nasir Zadeh wanda yake ziyara a kasar Syria ya gana da shugaba Basshar Asad inda su ka tattauna batun tsaro da

Ministan tsaron Iran  Azizi Nasir Zadeh wanda yake ziyara a kasar Syria ya gana da shugaba Basshar Asad inda su ka tattauna batun tsaro da halin da ake ciki a wanann yankin na yammacin Asiya, da kuma hanyoyin aiki a tsakanin kasashen biyu wajen fada da ta’addanci.

Shugaba Basshar Asada ya bayyana cewa kawo karshen ta’addanci wani nauyi ne wanda ya rataya a wuyan kasashen wannan yankin da kuma duniya baki daya, domin hatsarinsa zai shafi kowa da kowa.

A jiya Asabar ne dai ministan tsaron na Iran ya isa birnin Damascuss, inda ya gana da manyan jami’an wannan kasar da su ka hada da takwaransa na Syria.

Ministan tsaron na Iran ya fada wa taron manema labaru cewa; Kasar Syria tana da matukar muhimmanci a cikin siyasar waje ta jamhuriyar musulunci ta Iran, wannan ne ya sa nake ziyartar Syria domin amsa goron gayyatar ministan tsaronta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments