Ministan Tsaron Iran Ya Ce Suna Goyon Bayan Kasar Siriya Dari Bisa Dari

Ministan tsaron Iran ya bayyana cewa: Kasarsa tana goyon bayan kasar Siriya dari bisa dari bisa umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci A zantawarsa da

Ministan tsaron Iran ya bayyana cewa: Kasarsa tana goyon bayan kasar Siriya dari bisa dari bisa umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci

A zantawarsa da manema labarai a birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya, Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya bayyana cewa: Kasar Siriya na taka muhimmiyar rawa a fagen siyasar kasar Iran kuma za su ba ta cikakken goyon baya bisa umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar.

Ministan tsaron kasar Iran ya isa birnin na Damascus fadar mulkin kasar Siriya ce a yau Asabar, inda ake sa ran zai gana da shugaban kasar Bashar Asad da takwaransa na Siriya tare da tattaunawa da su kan batutuwan da suka shafe kasashen biyua fagen yanki da na kasa da kasa.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan karfafa alaka da bunkasa matakan harkokin tsaron kasashen biyu, tare da jaddada muhimmiyar rawar da kasashen yankin ke takawa wajen samar da tsaro, da wajibcin ficewar sojojin kasashen waje daga yankin, da ci gaba da gudanar da taimakekkeniya a tsakaninsu don tunkarar nau’o’in ta’addanci daban-daban, da kuma tattaunawa a fagen ci gaban yankin da kuma goyon bayan gwagwarmayar al’umma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments