Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta sanar da cewa; A ranar Litinin mai zuwa minister Segey Lavrov zai kawo ziyarar aiki zuwa Iran domin tattauna hanyoyin da su ka shafi kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a wannan yankin.
Sanarwar ta ce Sergey Lavrov zai ziyarci Iran a ranar 19 ga watan nan na Oktoba zai kuwa gana da takwaransa na Iran Abbas Arakci.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ce ta sanar da hakan a jiya Juma’a sannan ta kara da cewa; manufar ziyarar ita ce kokarin da Rasha take yin a rage zaman zullumi da ake da shi a yankin,sannan kuma da aiwatar da yarjeniyoyin a aka kulla.
Zakharova ta kuma ce; Daga cikin batutuwan da bangarorin biyu za su tattauna da a kwai yarjeniyoyin aiki tare a cikin muhimman manufofi na koli a tsakanin Tehran da Moscow.