Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana babbar manufar aiwatar da kisan gilla kan Isma’il Haniyeh a cikin kasar Iran
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya yi nuni da cewa: Iran ta ki amincewa da tada zaune tsaye, da shiga cikin manyan ayyukan soji, kuma kisan Isma’il Haniyeh wani yunkuri ne na tada hankalin Iran.
Lavrov ya ce a cikin wata hira da tashar Russian Today ya bayyana cewa: “Suna kokarin tada hankalin Iran ne, kuma shi ne ya sa suka kashe shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Isma’il Haniyeh a babban birnin Tehran.”
Lavrov ya jaddada a lokuta da dama cewa: Iran ta kin amincewa da yunkurin dora mata alhakin komai, don haka wadannan abubuwan da suke faruwa yunƙuri ne na tayar da hankalinta.
Ya ce: “Hadarin rikicin Gaza na iya rikidewa zuwa rikici a dukkan yankin Gabas ta Tsakiya da zai iya yin matukar muni.”
Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya jaddada cewa: Ya yi imanin cewa, shugabancin Iran yana daukar wani matsayi na kwarai da daidaito, da kuma yin kira da a hana yaduwar wannan rikici a yankin.