Ministan Harkokin Wajen Kasar Jamus Ta Ce Hare Haren Beirut Zai Kara Rikita Harkokin Tsaro A HKI Ne Kawai

Ministan harkokin wajen kasar Jamus Annalena Baerbock ta bayyana cewa hare haren da HKI take kaiwa a kasar Lebanon za su kara rikita harkokin tsaro

Ministan harkokin wajen kasar Jamus Annalena Baerbock ta bayyana cewa hare haren da HKI take kaiwa a kasar Lebanon za su kara rikita harkokin tsaro a cikin HKI ne kawai.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Baerbock tana fadar haka a jiya Asabar ta kuma kara da cewa  “akwai barazanar rikita kasar Lebanon, sannan ya kara rikita harkokin tsaro a HKI.

Ministan ta bayyana haka ne bayan hare haren da jiragen yakin HKI suka kai kan kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon wanda ya kai ga shahadar shugaban kungiyar Hizbulla Sayyid Hassan Nasarallah tare da wadanda suke tare da shi.

Tace sojojin HKI, sun kai hare haren ne bayan da kasashen Amurka, Faransa da kuma Jamus suka gabatar da shawarar tsagaita wuta na kwanaki 21 tsakanin kungiyar da kuma HKI.

Ministan ta kammala da cewa al-amura a yankin suna da matukar hatsari, don akwai yiyuwar yakin ya kara fadada. Banda haka ta bayyana cewa rikita kasar Lebanon zai sa yahudawa kimani 80,000 da suka kauracewa gidajensu a arewacin HKI su kasa komawa gidajensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments