Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yace Asasin Yarjeniyar Kasar Da Rasha Ta Tattalin Arziki Ne

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa asasin yarjeniya ta musamman da kasar Rasha ta tattalin arziki ne. Wadanda suka hada da

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa asasin yarjeniya ta musamman da kasar Rasha ta tattalin arziki ne. Wadanda suka hada da manya-manyan al-amuran tattalin arziki kamar Makamashi, Sifili, da yawon shakatawa da kuma kasuwanci.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana cewa yarjeniyar ta hada kome da kome, amma akwai wadanda za’a fi kula da su daga lokaci zuwa lokaci. Yace wannan yarjeniyar ta zo ne a dai-dai lokacinda kasashen biyu suke fama da matsalolin tattalin arziki sanadiyyar takunkuman tattalin arziki daga kasashen yamma.

Yace kafin haka ma, dangantakar kasashen biyu yana da karfi, amma samun wannan yarjeniyar ya kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments