Ministan Harkokin Wajen Iran Yace Faransa Bata Da Yencin ZarginWata Kasa Dange Da Kare Hakkin Bil’adama

Mainistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Faransa bata da hakkin sukar wata kasa a duniya dangane da abinda ya

Mainistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Faransa bata da hakkin sukar wata kasa a duniya dangane da abinda ya shafi kare hakkin bil’adama. Bayan matsayinta a kissan kiyashin da HKI take aikatawa a gaza.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministan yana maida martani ne ga tokwaransa na kasar Faransa Jean-Noel Barrot ya fada bayan da wani ba’irane ya sami lambar yabo mafi girma a gasar fina-fina mafi girma a duniya da ake kira ‘ Cannes Film Festival’ . Jafar Panohi dan kasar Iran ya lashe kyauta mafi girma a gasar ne saboda wani film da ya yi, wanda ya bashi makin samun wannan kyautar.

Aragchi ya bayyana cewa, Faransa ta tabbatar da cewa kare hakkin bil’adama idan ya shafi kawarsu HKI ce , kissan Falasdinawa 56,000 kare kaine amma ba’ira ne ya ci lamba mafi girma bai dace ba don kasarta tana take hakkin bil’dama. Wannan shi ne fuska biyu a mizanin kare hakkin bil’adama a wajen kasar farsanda da kasashen yamma da dam.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments