Search
Close this search box.

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Nufi Gambia Domin Halartar Taron Kungiyar OIC Karo Na 15

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya bar birnin Tehran zuwa Banjul babban birnin kasar Gambia domin halartar taron kolin kungiyar hadin kan kasashen

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya bar birnin Tehran zuwa Banjul babban birnin kasar Gambia domin halartar taron kolin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC karo na 15.

Amir Abdollahian wanda ya jagoranci wata babbar tawaga, ya tashi zuwa birnin Banjul a ranar Juma’a domin halartar taron, wanda zai gudana a ranakun 4-5 ga wannan wata na Mayu.

Za a gudanar da zaman ne karkashin taken “Hadin kai ta hanyar tattaunawa don samun ci gaba mai dorewa”. Mahalarta taron za su tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi al’ummar musulmi, ciki har da abubuwan da suke faruwa a Falasdinu, musamman yakin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza.

Gabanin taron dai an gudanar da taron share fage ne a ranakun 30 ga Afrilu da 1 ga watan Mayu, inda manyan jami’an kungiyar OIC suka tattauna kan takardun zaman tare da mika rahotonsu ga taron share fage na majalisar ministocin harkokin waje na kasashen OIC.

Ministan harkokin wajen na Iran yana shirin bayyana matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran game da batutuwan da suka shafi kasashen musulmi da kuma halin d ake cikin a yankin gabas ta tsakiya, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa.

Taron na 15 zai fitar da sanarwar karshe da ta kunshi matsayar kungiyar OIC kan batutuwan da aka mika wa taron, da wani kuduri kan Palastinu da Quds.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments