‘Yan gwagwarmayar kasar Yemen sun harbo wani jirgin yakin Amurka yayin da yake kai hare-haren wuce gona da iri kan lardin Ma’arib na kasar
Dakarun kasar Yemen sun sanar da cewa: Dakarun tsaron saman kasar sun samu nasarar harbo wani jirgin saman yakin Amurka samfurin MQ9 a yammacin ranar Alhamis, a lokacin da yake kaddamar da wani mummunan hari a sararin samaniyar lardin Ma’arib da ke shiyar arewa maso gabashin birnin Sana’a fadar mulkin kasar ta Yemen.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar Sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya fitar a jiya Juma’a ya tabbatar da cewa: Wannan shi ne karo na hudu da suka harbo jirgin saman yakin makiya a jihadi mai tsarki da suke gudanarwa domin goyon bayan al’ummar Gaza.