Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kungiyar Hamas za ta ci gaba da tafiya da karfi fiye da a baya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Kungiyar Hamas tana da karfin gaske fiye da kowane lokaci, kuma za ta ci gaba da tafiya a kan tafarkinta fiye da na baya.
Wannan ya zo ne a cikin wata sanarwa da Araqchi ya fitar daga birnin Istanbul na kasar Turkiyya, inda ya kara da cewa: Sun gudanar da tattaunawa mai tsayi tare da abokai a majalisar shawara ta siyasa ta kungiyar Hamas, kan halin da ake ciki a Gaza, musamman tattaunawar tsagaita bude wuta da sauran batutuwan masu muhimmanci.
Araqchi ya ci gaba da cewa: Kowa ya sani cewa bayan shahadar Yahya Al-Sinwar da wasu da dama a Gaza, Hamas tana nan tsaye da karfinta, ita ce kashin bayan Falasdinawa kuma babu wanda zai yi musun matsayi da kimarsu a fagen kare al’ummarsu.