Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce Za Su Mayar Da Martani Matukar Hukumar IAEA Ta Kakaba Mata Takunkumi

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Iran za ta dauki sabbin matakai idan kwamitin Alkalan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Iran za ta dauki sabbin matakai idan kwamitin Alkalan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya fitar da wani kuduri kan kasarta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take don yin shawarwari kan batun Shirin makamashin nukiliyarta na zaman lafiya, amma a lokaci guda kuma ya bayyana cewa: “Idan kwamitin Alkalan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta fitar da wani kuduri kan Iran, to za su dauki sabbin matakai da ba za su yi daɗi ga hukumar ba.

Dangane da ziyarar da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi ya kai birnin Tehran a baya-bayan nan da kuma ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar ta Iran Araqchi ya ce: Mu’amalar Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya tana gudanar cikin kyakkyawan yanayi, amma dole ne hukumar ta IAEA ta gudanar da ayyukanta a fagen fasaha, kuma ba ta da hakkin shiga fagen siyasa, don haka muddin hukumar tana gudanar da aikinta cikin kwarewa, to Iran za ta bada cikakken hadin kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments