Miliyoyin Iraniyawa Ne Suka Halarci Jana’izar Shugaba Raeisi, Da Mukarabansa

A Iran, miliyoyin mutane ne suka halarci jana’izar shugaban kasar Iran Ebrahim Raeisi da mukarabansa da suka yi shahada a wani hatsarin jirgin sama mai

A Iran, miliyoyin mutane ne suka halarci jana’izar shugaban kasar Iran Ebrahim Raeisi da mukarabansa da suka yi shahada a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin kasar.

An fara bikin jana’izar ne a safiyar yau Talata a yankin Tabriz, inda aka samu dimbin jama’a galibi sanye da bakaken tufafi, suna zagaye da akwatunan gawarwakin, dauke da tutar kasar da hotunan shahiddan.

Da yake jawabi a wajen a birnin Tabriz, ministan harkokin cikin gidan kasar Ahmad Vahdidi ya ce Iran na jimamin rashin shugaban kasa mai kaunar jama’a, mai farin jini kuma mai tawali’u.

M. Vahidi ya kara da cewa al’ummar Iran suna bakin ciki da rasuwar shi ma ministan harkokin wajen kasar wanda ya bar aikin diflomasiyya a cikin hali na tsayin daka.

Ya kuma yaba da irin kokarin da marigayi gwamnan lardin Azarbaijan ta gabas da kuma Limamin masallacin sallar Juma’a na lardin ya yi.

“Mun yi rishi babba a wannan lamarin, amma za mu sami babban ci gaba,” in ji Vahidi.

An kuma gudanar da wani taron jana’izar shugaba Raeisin da mukarabansa a birnin Qom da ke arewa ta tsakiyar kasar, sannan an iso da gawawakin nan Tehran babban birnin kasar domin yin wata jana’izar ranar Laraba.

Za’a binne shugaban kasar mai rasuwa a yankin Mashhad inda cen ne mahaifarsa.

Jirgin mai saukar ungulu dauke da Raisi da tawagarsa ya yi hadari ne da yammacin ranar Lahadi a kan hanyarsa ta zuwa Tabriz babban birnin lardin Azarbaijan na kasar Iran a gabashin kasar, inda shugaban kasar ya halarci bikin bude madatsar ruwa a iyaka da kasar Azerbaijan tare da takwaransa Ilham Aliyev.

Masu aikin ceto sun gano tarkacen jirgin mai saukar ungulu da sanyin safiyar ranar Litinin bayan shafe sa’o’i ana nema.

Ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian da wasu gwamnan lardin Azerbaijan da Limamin Juma’a na yankin Tabriz tare da ma’aikatan jirgin da masu gadi su ma sun yi shahada sakamakon hadarin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments