Mikati: Ba Za Mu Yarda Da Cigaba Da Zaman Sojojin “ Isra’ila” A Lebanon Ba Bayan Kwanaki 60 Na Tsagaita Wutar Yaki

Shugaban gwamantin kasar ta Lebanon Najib Mikati ya fada wa dan sakon Amurka Amos J. Hochstein cewa, Lebanon ba za ta aminta da cewa sojojin

Shugaban gwamantin kasar ta Lebanon Najib Mikati ya fada wa dan sakon Amurka Amos J. Hochstein cewa, Lebanon ba za ta aminta da cewa sojojin mamayar HKI su cigaba da zama a cikin kasar ba, bayan gushewar kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki.

Shugaban  gwmanatin kasar ta Lebanon ya fada wa dan sakon na Amurka cewal wajibi ne su tilasta wa Isra’ila ta daina keta tsagaita wutar yaki.”

Haka nan kuma ya kara da cewa, cigaban keta yarjejeniyar wutar yakin bayan cikar kwanaki 60 ba abu ne da za a lamunta da shi ba, sannan kuma ya kara da cewa; Muna gabatarwa da kasashen da suke kula da tsagaita wutar yakin abinda yake faruwa.

Haka nan kuma ya bukaci ganin an fito da jadawalin ficewar sojojin na ‘yan mamaya gabanin kwanaki 60 din su cika.

A ranar 27 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata ne dai aka fara aiki da tsagaita wutar yaki a tsakanin Lebanon da HKI, bisa cewa daga lokacin zuwa kwanaki 60 sojojin mamayar za su janye daga wuraren da su ka shiga.

Sai dai a cikin kwanakin nan jami’an HKI suna cewa ko bayan cikar kwanaki 60 ba za su fice daga inda su ka shiga ba.

Shugaban gwamnatin kasar ta Lenabon Najib Mikati, ya karbi bakuncin dan sakon Amruka a fadar gwmanati dake birnin Beirut inda su ka tattauna halin da ake ciki a kudancin Lebanon tun bayan tsagaita wutar yakin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments