MDD Ta Nuna Damuwarta Da Abinda ke Faruwa A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Kakakin babban sakataren MDD ya bayyana damuwarsa kan abubuwan da suke faruwa a yankin yamma da kogin Jordan, inda sojojin HKI suke ci gaba da

Kakakin babban sakataren MDD ya bayyana damuwarsa kan abubuwan da suke faruwa a yankin yamma da kogin Jordan, inda sojojin HKI suke ci gaba da rusa gidaje, da bata yanyuyi da kuma dukan Faladinawa da suka hadu da su a yankin arewacin yamma da kogin na Jordan.

Tashar talabijin ta Presstva anan Tehran ya nakalto Stephane Dujarric kakakin babban sakataren MDD yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa, wakilan Majalisar a yankun sun bada rahoton yadda sojojin HKI suka kutsa a cikin sansanin yan gudun hijira na al-Arroub wanda yake cikin yankin Shuyukh al-Arrub, inda suka daki wani matsayi da kasar bindiga har suka fasa masa bakinsa suka kuma karya masa kafa.

Har’ila yau rahoton ya kara da cewa yahudawan sun tilastawa falasdinawa da dama rufe shagunasu da kuma tserewa daga yankin, bayan da suka jefa masu hayaki mai sa hawaye, kuma dauki da guba..Kamfanin dillancin labaran WAFA ta Falasdinawa ya bada irin rahoto guda a yankin. Tun bayan dakarar da yaki a Gaza sojojin yahudawan sun karfafa ayyukan soje a yankin yamma da kogin Jordan da nufin korar Falasdinwa daga yankin kwatakwata

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments