MDD Ta Nuna Damuwa Akan Tabarbarewar Yanayin “Yan Hijira A Gabashin  Kasar Chadi

MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar

MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar da kudaden taimakon kula da su.

Ma’aikatan MDD a fagen ayyukan ceto sun ce ana samun kwararar ‘yan hijira daga Sudan zuwa gabashin kasar ta Chadi, da kuma ‘yan kasar ta Chadi da suke komawa gida.

Tun da yaki ya barke a Sudan zuwa yanzu an yi rijistar kwararar ‘yan Sudan masu yawa. A cikin wata daya kadai ‘yan Sudan  su dubu 55, sai kuma ‘yan asalin Chadi da su ka koma gida zuwa Jahar Inidy da yankin Fira, a gabashin kasar, da su kuma sun kai dubu 39.

Sanarwar ta MDD ta ci gaba da cewa; Wannan sabon adadin ya karu ne akan wasu ‘yan hijirar miliyan daya  da sun dade da shiga gabashin Chadi, tun daga fara yakin basasar Sudan a a tsakiyar watan Aprilu na 2023.

Mai Magana da yawun MDD Stephen Dujarric ya ce; siyasar da kasar Chadi take aiki da ita bude kofofinta ga ‘yan hijirar ne ya bayar da wannan damar.

Haka nan kuma ya bayyana cewa wuraren da aka ware domin tarbar ‘yan hijirar a gabashin Sudan din sun yi kadan’ sannan ya kara da cewa; mafi yawancin masu kwararowar mata ne da kananan yara da su ka kadu saboda yakin da ake yi a can Sudan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted