Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Isra’ila da ta ba ta damar shiga zirin Gaza domin kai kayan agaji ga yankin da aka yi wa kawanya.
Kakakin babban sakataren MDD ya fada a ranar Juma’a cewa bisa ga dokokin jin kai na kasa da kasa, dole ne a bar fararen hula su sami taimako a duk inda suke.
Stephane Dujarric ya ce mahukuntan Isra’ila na ci gaba da watsi da bukatar shiga asibitocin da ke arewacin Gaza.
A cewar Dujarric a makon da ya gabata, an toshe dukkan yunkurin tura tawagar likitocin gaggawa ta kasa da kasa a cikin asibitoci.
Arewacin Gaza dai ya shafe fiye da wata guda yana karkashin kawanya kuma an umarci mutanen wurin da su kaura.
Sai dai kuma Falasdinawa da ke kokarin zuwa kudancin Isra’ilan na fuskantar hare-haren sari-ka-noke da jirage marasa matuka.