Hukumar kula da samar da agaji ta MDD OCHA ta bada sanarwan kissan Falasdinawa fiye da 100 a lokacinda suke kokarin neman abincin da zasu ci.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin shugaban kungiyar ta OCHA Farhan Haq yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa bai kamata mutane sum utu a wajen neman abinci ba. Dokokin kasa da kasa sun tabbatar da cewa, mutum ko menene laifinsa bai kamata a hana shi abinci ba, kuma bai kamata yam utu saboda neman abinci ba.
Farhan Haq ya yi gargadin cewa idan wannan halin ya ci gaba, to dukkan duniya sun ji kunya, idan suna da shi, suna ganin Falasdinawa suna mutuwa a lokacinda kowa a duniya yana kallo, amma ba wanda ya isa ya hana hakan faruwa.
Yace kofar ragon da HKI ta yiwa Gaza, ya kai ga a halin nyanzu yunwa ta yi tsanani a gaza ta yadda yuwan tana kashesu a mazauninsu a cikin gaza. Kuma maganin shi ne dole ne a cika gaza da kayakin abinci.