MDD : Adadin Falasdinawa Da Suka Yi Gudun Hijira A Yammacin Kogin Jordan Ya Ninka

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ta ce adadin Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a yammacin gabar kogin Jordan da

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ta ce adadin Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye ciki har da gabashin birnin Kudus, ya ninka fiye da ninki biyu tun a ranar 7 ga watan Oktoba idan aka kwatanta da watanni 10 da suka gabata.

OCHA ta ce Falasdinawa 3,070 ne aka tilastawa barin gidajensu saboda rugujewa, tashin hankali da kuma kwace musu filaye a cikin watanni 10 da suka gabata, idan aka kwatanta da 1,252 a baya.

Hukumar ta kara da cewa kimanin mutane 181,000 a Yammacin Kogin Jordan na fuskantar matsalar, ruwa da tsaftar muhalli, da sauran ababen more rayuwa tun ranar 7 ga watan Oktoba, musamman a lokacin farmakin da sojojin Isra’ila suka kai a Tulkarem da Jenin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments