Matsaloli A Kamfanin Microsoft Ya Haddasa Rufewar Miliyoyin Kumfutoci A Duniya

Wata matsala da ta taso a kamfanin Microsoft wanda yake kula da manhajar ‘windows’ ya haddasa matsaloli da dama a duniya a jiya jumma’a. Matsalolin

Wata matsala da ta taso a kamfanin Microsoft wanda yake kula da manhajar ‘windows’ ya haddasa matsaloli da dama a duniya a jiya jumma’a. Matsalolin da suka sa miliyoyin kumfutici suka rufe kawukansu, a tashoshin jirahen sama, tashoshin talabijin, asbitoci da wurare da dama, kama daga Australia, New Zealand, India, Japan, Burtaniya da kuma Amurka inda kamfanin yake.

Wasu kafafen yada labarai sun nakalto kamfanin Microsoft yana cewa matsalat daga wajensu ne, kuma sun yi kokarin sanya wani sabon ‘Anti Virus’ ne a cikin manhajar window wanda ya jawo wannan matsalar.

A wasu kasashen dai an fara gyaran kumfutocin da hannu, sannan wasu shaguna sun dawo da saya da sayarwa da hannu ko na’urar lissafi.

Kamfanin Microsoft ya bada sanarwan cewa yana saran nan bad a dadewa ba zasu shawo kan matsalar. A nan kasar Iran dai babu wani kumfuta da ya fuskanci wannan matsalar saboda dama Amurka ta dodeta daga amfani da kayakin Microsoft da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments