Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya?
Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar.
Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa, gobara mai karfin gaske ta barke a tsaunukan birnin Kudus ta kuma bazu zuwa manyan yankuna masu girma.
Gobarar ta tashi ne a kusa da babbar hanyar da ke tsakanin Kudus da Tel Aviv, lamarin da ya kawo yawaitar cunkoson ababen hawa a manyan tituna. Gobarar ta yi sanadin jikkatar mutane masu yawa, kuma ta tilastawa hukumomin gwamnatin mamaya fara kwashe yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida daga gidajensu da ma marasa lafiya daga Asibitin Hadassah Ein Kerem da ke birnin Kudus saboda gobarar.