Masar ta jaddada goyon bayanta ga zaman lafiyar Sudan tare da yin watsi da matakan bangare guda kan kogin Nilu
Kasar Masar ta jaddada cikakken goyon bayanta ga zaman lafiyar kasar Sudan da kuma yankinta a jiya Laraba, tare da tabbatar da hadin kan matsayar kasashen biyu da kuma kin amincewa da matakan bangare daya kan kogin Nilu.
Wannan dai ya zo ne a wata ganawa da ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty da shugaban majalisar gudanar da mulkin Sudan Abdel Fattah al-Burhan suka yi a birnin Port Sudan, a cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar.
Abdel Aty ya ce ziyararsa ta uku zuwa Port Sudan cikin shekara guda sako ne na nuna goyon baya ga Sudan a cikin mawuyacin halin da kasar ke ciki. Ya tabbatar da cikakken goyon bayan Masar ga Sudan da kuma goyon bayanta ga zaman lafiyarta, tsaro, ikonta, cikakken yankinta, da cibiyoyin kasa, musamman rundunar sojojin Sudan.
Ministan harkokin wajen kasar Masar ya jaddada aniyar kasarsa na yin taka-tsan-tsan a kokarin da ake na cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Sudan, da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da kuma kawo karshen radadin da al’ummar Sudan ke ciki.