Wani masanin harkokin siyasa ya bayyana kisan babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah a matsayin wata nasara da ba ta amfani ga yahudawan sahayoniyya
Marubuci kuma masanin harkokin siyasa Hassan Shuqair ya bayyana kisan da aka yi wa babban sakataren kungiyar Hizbullah, shahidi Sayyid Hassan Nasrallah, a matsayin wata nasara da ba za ta yi amfani ga fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, saboda hakan zai sanya janyo nasarar dabarar ‘yan gwagwarmaya a yakin da suke yi da ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya.
A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam ta kasar Iran, Hassan Shuqair ya ce: Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu a baya ya dora tunaninsa kan cewa ta hanyar kaskanta Nasrallah, zai iya tilasta Sinwar ya durkusa ya amince da yarjejeniyar musayar fursunoni kan sharuddan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, to, hakan rudun tunani ne da rashin sanin tushen gwagwarmaya.
Shuqair ya kara da cewa: Hakika sakamakon shahadar Sayyed Nasrallah kungiyar Hizbullah za ta kara karfi fiye da yadda ake tsammani, matakin kwamawarta zai kara tsananta, kuma mayakanta za su kara zage dantse a fagen yaki gadan-gadan, don haka kungiyar Hizbullah ba za ta yi kasa a gwiwa ba don babban sakatarenta ya yi shahada, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa a yi nasara kanta ba, kuma za ta ci gaba da yaki ba kama hannun yaro, saboda haka, Yahya Sinwar ba zai yi kasa a gwiwa ba, kuma ba zai mika fursunoni yahudawan sahayoniyya kan sharuddan ‘yan mamaya ba, kuma gaba dayan iyalan fursunoni da magoya bayansu a haramtacciyar kasar Isra’ila za su koma tambayar Netanyahu ina fursunoni suke kuma a ina aka yi musayar fursunoni?