Manyan Jami’ai A Kasashen Turai Sun Fara Dawowa Daga rakiyar Isra’ila

Jami’ai uku na yammacin Turai sun sanar da matsayinsu na kyamar zaluncin Isra’ila kan al’ummar Falastinu musamman mazauna zirin gaza. Tun daga ranar 7 ga

Jami’ai uku na yammacin Turai sun sanar da matsayinsu na kyamar zaluncin Isra’ila kan al’ummar Falastinu musamman mazauna zirin gaza.

Tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 tare da cikakken goyon bayan Amurka da wasu kasashen yammacin turai gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta fara kaddamar da  gagarumin kisan gilla a zirin Gaza da yammacin gabar kogin Jordan kan al’ummar Palastinu marasa kariya da ake zalunta,

A cewar shafin Pars Today, Mark Smith, jami’in da ke kula da ofishin jakadancin Burtaniya a Dublin, babban birnin kasar Ireland, ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Lahadin da ta gabata, don nuna adawa da matakin da London ta dauka na kin hana fitar da makamai zuwa Isra’ila, ya kuma ce: Manyan jami’an  sojojin Isra’ila da gwamnati da sauran bangarorin tsaronta a fili suna neman yin kisan kare dangi a Gaza.”

Smith ya yi nuni da cewa motocin daukar marasa lafiya, makarantu da asibitocin da ke da alaka da kungiyar agaji ta Red Cross a Gaza ana kai hare-hare kansu kai-akai, ya kara da cewa: “farar hula ba su da inda za su je.”

A halin da ake ciki, magajin garin Chicago Brandon Johnson, ya bayyana yakin da gwamnatin sahyoniyawan ke yi a Gaza a matsayin kisan kare dangi, ya kuma ce abin da ke faruwa a Gaza abin kunya ne ga ita kanta Isra’ila da kuma sauran gwamnatocin kasashen duniya da suka kasa taka ma Isra’ila Burki.

Mike Wallace mamba a majalisar kungiyar Tarayyar Turai,  ya saka hotonsa rike da tutar Falasdinu a wani filin wasa, ya kuma ce: Aikin mulkin mallaka na yahudawean  Sahayoniyya da magoya bayansu a Gaza, yana kasancewa fili tare da cikakken goyon bayan Amurka da kungiyar Tarayyar Turai, kuma babu wani mai musun hakana a duniya.

Ta hanyar amfani da taken #FreePalestine, mamban na majalisar kungiyar Tarayyar Turai ya yi jawabi ga gwamnatin Isra’ila da magoya bayanta: “Ku Dakatar da kisan kare dangi.”

Shi dai wannan dan kasar Ireland a majalisar dokokin tarayyar turai, wanda ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da yahudawan sahyoniyawan suke yi a Gaza, a baya ya bayyana Isra’ila a matsayin ‘yan ta’adda, tare da bayyana abin da suke yin a kisan Falastinawa da ayyukan ta’addanci.

A baya Mike Wallace ya kwatanta masu goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan da magoya bayan jam’iyyar Nazi, wadanda suka yi mulkin kama karya a Jamus a karakshin jagorancin babban shugabansu Adolf Hitler, ya kuma ce: Isra’ila ba ta mutunta dokokin kasa da kasa.

Rahotanni na baya-bayan nan na cewa, sama da Falasdinawa dubu 40 ne aka kashe tare da jikkata wasu fiye da 92,000 a hare-haren da gwamnatin yahudawan sahyuniya ke kaiwa Gaza.

An kafa gwamnatin Isra’ila a shekara ta 1917 ta hanyar tsarin mulkin mallaka na Birtaniya da kuma ta hanyar kwaso yahudawa masu yin hijira daga kasashe daban-daban zuwa yankunan Falasdinu, kuma an sanar da wanzuwarta a shekara ta 1948.

Tun daga wannan lokacin ne aka fara aiwatar da tsare-tsaren kisan gilla daban-daban domin kakkabe Falasdinawa tare da kwace dukkan filayensu.

Abin da Isra’ila take yi a halin na kisan kare dangi a yankin zirin Gaza da kuma wasu yankuna na gabar yammacin kogin Jordan, duk wani tsararren lamari ne wanda aka shirya tun daga lokacin da Burtaniya ta kafa Isra’ila.

Da dama daga cikin masana suna yin ishara da cewa, wasu mutane a duniya sun yaudaru da cewa Hamas c eta fara tsokanar Isra’ila ta hanyar kai harin daukar fansa a ranar 7 ga watan Oktoba wanda shi en ya jawo kisan kiyashin da Isra’ila take yia  halin yanzu a Gaza, alhali kuwa ba haka lamarin yake ba, tun daga lokacin da aka kafa Isra’ila shekaru 75 da suka gabata, tun daga lokacin yahudawa suke yi wa Falastinawa kisan gilla musamman yankin zirin gaza, saboda abin da ke faruwa a yanzu ya kara bayyana ne a fili ga duniya, sakamakon ci gaban zamani da saurin isar da sakonni ta kafofin sadarwa na zamani, da shafukan yanar gizo da sauran shafukan zumunta, wanda cikin kankanin lokacin abin da yafu kowa zai gani a duniya.

Tabbas abin dayak faruwa kamar yadda wadannan jami’ai uku da muka ambatasuka yi bayani, Amurka da tarayyar turai su ne kan gaba wajen bayar da goyon baya na siyasa da tsaro da tatallafa wa tattalin arzikin Isra’ila , wanda hakan ya bata ddamar ci gaba da aiwatar da abin da tke yia  halin yanzua  yankin zirin gaza, wanda kuma tabbas lokaci na zuwa wanda reshe zai juye da mujiya, kuma tun yanzu alamau sun fara nuna hakan, domin kuwa zanga-zangar la’antar Isra’ila dake a cikin kasashen turai hard a Amurka , ta fi wadda ake yia a ickin kasashen larabawa yawa da kuma tasiri, da isar da babban sako da ke nuni da cewa duniya ta gano wacece Isra’ila, dandazo ne na ‘yuan daba da makasa masha jinni, da sunan kasar yahudawa, kuma duniya za ta ci gaba da kallon Isra’ila a haka, wanda kuma daga karshe ko bade ko jima zalunci baya dawwama, gaskiya da adalci da rauanna ne suke yin gabalaba a kan masu girman kai da kama karya, kamar yadda kuma tarihin duniya ya tabbatar da hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments