Malaman Sunna sun bayyana godiya ga Jagora bisa mayar da martani kan Isra’ila

Kimanin malaman Sunna 3,000 ne suka rubutawa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei wasika, inda suke nuna godiya da goyon bayansu ga

Kimanin malaman Sunna 3,000 ne suka rubutawa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei wasika, inda suke nuna godiya da goyon bayansu ga aiwatar da farmakin da Iran ta yi  a baya-bayan nan kan yankunan Falasdinawa da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta mamaye.

A cikin wata wasika da suka aike wa Jagoran a wannan Litinin, malaman sun gode wa Ayatullah Khamenei saboda “karfin jagoranci mai hikima” da ya kai ga aiwatar da aikin da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar (IRGC) suka kaddamar.

Wannan farmakin ya nufi tsakiyar yankunan da aka mamaye tare da manyan makamai masu linzami, wanda hakan ya faranta ran dukkanin al’ummar musulmi.

A ranar Talata Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba makamai masu linzami 200 zuwa sansanonin soji da na leken asirin Isra’ila a duk fadin yankunan da ta mamaye a wani bangare na Operation True Promise II a matsayin mayar da martani ga mummunan harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai cikin Tehran da ya yi sanadin shahadar Isma’il Haniyya shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, da kuma kisan gillar da suka yi Sayyid Hassan Nasrallah babban sakataren kungiyar Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments