Majiyoyin Diblomasiyya Sun Ce Washington Zata Jagoranci Turawa A Tattaunawa Da Iran

Wasu kafafen diblomasiyya nakasashen yamma sun tabbatarwa wakilin tashar talabijin ta Al-mayadeen na kasar Lebanon kan cewa gwamnatin Amurka ce zata jagoranci kasashen yamma wajen

Wasu kafafen diblomasiyya nakasashen yamma sun tabbatarwa wakilin tashar talabijin ta Al-mayadeen na kasar Lebanon kan cewa gwamnatin Amurka ce zata jagoranci kasashen yamma wajen tattaunawa da karar Iran.

Majiyar ta kara da cewa turawan sun mika wuya ga takurawar washintong don jagorantar tattaunawa da JMI kan shirinta namakamashin nukliya da kuma batun yin watsi da sabon yarjeniyar da Iran ta kulla da hukumar IAEA a al-kahira a baya bayan nan.

Banda haka suna son suyi amfani da tsarin Snapbackdon  kara takurawa JMI. Sannan kasashen turaiba zasu sararawa JMI ko kadan ba a takurawar da suke mata a tattaunawar.

Duk da cewa yarjeniyar Al-kahiri wani bangaremai muhimmanci ne ga bukatun kasashen Turai daga Tehran, amma har yanzun akwai sabbin sharuddan da sabbon sharudda da zasu kara.

Sai dai a halin yanzun da tunda Amurkata dawo tana jagorantar kasashen na Turai, yiyuwar dawo dadukkan takunkuman MDD kan Tehran yana da karfi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments