Majiyar Rundunar Sojin Siriya Ta Karyata Rade-Radin Janyewar Sojojinta Daga Birnin Homs

Sojojin gwamnatin Siriya sun musanta rade-radin cewa sun janyewa daga birnin Homs Majiyar sojan Siriya ta bayyana cewa: Babu kanshin gaskiya kan rahotannin da aka

Sojojin gwamnatin Siriya sun musanta rade-radin cewa sun janyewa daga birnin Homs

Majiyar sojan Siriya ta bayyana cewa: Babu kanshin gaskiya kan rahotannin da aka wallafa a shafukan ‘yan ta’adda game da janyewar sojojin daga birnin Homs.

Majiyar soji ta jaddada cewa: Babu kanshin gaskiya kan rahotannin da aka wallafa a shafukan ‘yan ta’adda game da janyewar sojojin daga birnin Homs, tana tabbatar da cewa sojojin Larabawa na kasar Siriya suna nan a birnin Homs da kuma yankunansa, kuma an jibge su a kan yankuna masu tsaro da matakan kariya kuma an karfafa su da makamai masuinganci don kalubalantar ‘yan ta’adda. Kamar yadda aka kara karfafa su da yawan dakaru masu dauke da kayan yaki iri-iri da manyan  makamai, kuma dakarun suna shirye su dakile duk wani hari da ‘yan ta’adda zasu kai kan birnin.

Kamar yadda majiyar sojin ta Siriya ta sanar da cewa: Kungiyoyi masu dauke da makamai suna yada faifan bidiyo na karya da kage na fashe-fashe a hedkwatar rundunar soji da ke tsakiyar Damascus fadar mulkin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments