Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce: Za A Kashe Dala Biliya 53 Wajen Sake Gina Zirin Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Sake gina Gaza na bukatar kudi sama da dala biliyan 53 Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya ya fada

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Sake gina Gaza na bukatar kudi sama da dala biliyan 53

Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya ya fada a ranar Talata cewa: Sake gina yankin Zirin Gaza da yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya lalata yana bukatar kudi sama da dala biliyan 53, ciki har da sama da dala biliyan 20 cikin shekaru uku na farko.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya rubuta a cikin wani rahoto da aka shirya bisa bukatar babban zauren Majalisar Dinkin Duniya cewa: Adadin kudaden da ake bukata don farfado da sake gina yankin a cikin gajeren lokaci, matsakaita da kuma dogon lokaci a Zirin Gaza “an kiyasta kimanin dala biliyan 53 da miliyan 142. A cikin wannan adadin, an kiyasta kudaden da ake bukata a cikin gajeren lokaci na shekaru uku na farko da kusan dala biliyan 20 da 568.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments