Search
Close this search box.

Maida Martani Hizbullah Kan HKI Mai Suna ’40’ Yana Da Tsanani Amma HKI Tana Boyewa

Shugaban makarantar sojoji na kasar Iran ya bayyana cewa maida martanin da dakarun kungiyar Hizbullah suka kai kan HKI saboda kisan Sayyid Fu’ad Shukur daya

Shugaban makarantar sojoji na kasar Iran ya bayyana cewa maida martanin da dakarun kungiyar Hizbullah suka kai kan HKI saboda kisan Sayyid Fu’ad Shukur daya daga cikin kwamandojin kungiyar wanda HKI ta kashe a Beirut ya na da natukar tsanani, Amma gwamnatin HKI ta hana a watso kome dangane da asarorin da HKI ta yi saboda farmaki na ’40’.

Kamfanin dill;ancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto kammafanin dillancin Mehr na kasar Iran na cewa, Janar Ahmad Mukaddam ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da kamfanin dillancin labaran Mehr yayi da shi.

Dangane da kissan Isama’ila Haniyyar shugaban kungiyar Hamas a Tehran kuma, Janar Mukaddam ya bayyana cewa kamar yadda jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Kahamae ya fada, maida martini kan kissan Haniya tabbas ne amma tare da samun dama mai kyau don maida martini.

Janar Mukaddam ya bayyana cewa HKI zata ji jiki a duk lokacinda JMI ta maida martani, kuma ya zama wajibi ko dole gareta ko kuma hakkinta ne ta maida martani a kan hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments