Mahmud Abbas:  Isra’ila Ba Ta Cancanci Zama Memba A MDD Ba

Shugaban gwamnatin kwarya-kwarya ta Falasdinu Mahmud Abbas ya bayyana cewa: Ko kadan bai kamata ace an bai wa Isra’ila kujera a MDD ba, domin abinda

Shugaban gwamnatin kwarya-kwarya ta Falasdinu Mahmud Abbas ya bayyana cewa: Ko kadan bai kamata ace an bai wa Isra’ila kujera a MDD ba, domin abinda take yi a Gaza kisan kiyashi ne.

Mahmud Abbas wanda ya gabatar da jawabi a taron MDD karo na 79 ya ce; Gwamnatin Falasdinu za ta gabatar da bukata a gaban MDD domin a dakatar a Isra’ila a matsayin memba, har zuwa lokacin da za ta yi aiko da dukkanin dokokin kasa da kasa.

Shugaban gwamnatin kwarya-kwaryar ta Falasdinu ya bayyana Isra’ila a matsayin fandararriyar kasa,tare da bukatar da kawo karshen laifukan yakin da take tafkawa. Haka nan kuma Mahmud Abbas ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa da su fara kakaba wa Isra’ila takunkumi  wacce ta rusa yankin Gaza da lalata duk wani abu da zai sa a iya rayuwa a cikinsa.

Wani sashen na jawabin shugaban na Falasdinawa, ya soki Amurka saboda yadda take goyon bayan HKI take kiyayya da al’ummar Falasdinu da hana su hakkokinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments