Shugabannin kasashen Amurka, Masar,Katar da Turkiya da su ka halarci taron na “ Herm-Sheikh” a kasar Masar sun sanya hannu akan yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a Gaza.
A jiya Litinin ne dai aka bude taron na Kasar Masar, wanda kuma ya sami halartar Fira ministan kasar Pakistan da kuma shugaban kasar Faransa.
Da yake gabaatar da jawabi, shugaban kasar Amurka Donald Trump yarjejeniyar ta zaman lafiya ta kunshi bangarori da dama, kuma tana tattare da ka’idojin aiwatar da ita.
Akan gawawwakin fursunonin Isra’ilawa, shugaban kasar ta Amurka ya ce ba a kai ga warwarewa ba baki daya, domin har yanzu ana ci gaba da kokarin gano inda suke.
Shi kuwa mai masaukin baki, Shugaban kasar Masar Abdulfattah al-Sisi, ya bayyana cewa; Yarjejeniyar ta Gaza za ta bude wani sabon shafin zaman lafiya a gabas ta tsakiya. Haka nan kuma ya ce; Kafa wa Falasdinawa kasa zai jaddada zaman lafiya.
Shugaban na kasar Amurka ya kuma ce; kasarsa za ta yi aiki kafada da kafada da Amurka da kuma sauran kawayenta domin sake gina yankin na Gaza.
Shi kuwa Fira ministan kasar Pakistan ya yi maraba da shirin zaman lafiyar da ya kawo karshen yakin Gaza.