shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, Aikewa da sojojin ruwan Amurka a yankin Caribbean itace barazana mafi girma ga al’ummomin yankin a cikin wannan karni.
Da yake magana a wani taron manema labarai, Maduro ya ce an jibge jiragen ruwan sojan Amurka guda 8 dauke da makamai masu linzami 1,200 da kuma na nukiliya a gabar tekun Venezuela. Inda Ya kira wannan matakin da cewa shi ne mafi muni da Amurka ta dauka a tsawon shkaru a yankin Caribbean.
Maduro ya zargi Washington da aiwatar da manufar matsin lamba ta soja a kan Caracas, wanda ya tilasta wa Venezuela ayyana cikakken shirin tsaron kasa.
“Venezuela kasa ce mai zaman lafiya, amma al’ummarta mayaka ne kuma ba za su taba yin watsi da barazana ko cin zarafi a kan kasarsu ba,” in ji shugaba Maduro.
A cikin watan Agustan 2025, Washington ta tura wasu manyan jiragen ruwa masu daukar makamai masu linzami guda uku, wato USS Gravely, USS Jason Dunham, da USS Sampson, kusa da yankin ruwan Venezuelan. Tare da sojoji da yawansu ya kai 4,000, lamarin da ya fuskanci tofin Allah tsine a fadin Latin Amurka.