Jaridar Maariv ta HKI ta buga wani rahoto wanda yake cewa; Sojojinsu suna fuskantar wahala mai tsanani a Kudancin Lebanon saboda suna da karancin sojojin sa-kai.
Rahoton ya ambaci cewa ana samun raguwar masu shiga cikin soja da hakan yake a matsayin matsala mai grima, domin zai yi tasiri a fadan da ake yi da Hizbullah.
Gabi Ashkenazi wanda tsohon janar ne na soja, kuma dan siyasar sahayoniya, ne ya shaida wa jaridar ta “Ma’arif” haka yana mai kara da cewa; Sojojin Isra’ila suna da masaniya akan cewa a cikin yanayi irin wannan na rashin masu shiga soja, za a sami koma bayan matsin lambar da ake yi wa kungiyar Hizbullah.
Ashkenazi ya kuma ce wasu daga cikin sojojin da suke yaki a yanzu sun dauki kwanaki 250 a filin daga ko ma fiye da hakan da hakan yake haddasa matsala a gare su ta fuskar tattalin arzkiki da kuma iyali.