Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da maganganun shugaban kasar Amurka Donal Trump a cikin majalisar dokokin HKI a jiya Litinin inda ya

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da maganganun shugaban kasar Amurka Donal Trump a cikin majalisar dokokin HKI a jiya Litinin inda ya bayyana cewa HKI ta sami nasara a yakin da ta kaiwa JMI a cikin watan Yunin da ya gabata, sannan daga karshe ya ce akwai bukatar a cimma yarjeniya da JMI kan shirinta na makamashin Nukliya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na cewa jawabin Trump a majalisar Knesset jawabi ne wanda bai da wani kima. Musamman a lokacinda yake gabatar da ita a gababan yan ta’adda makasa.

Ma’aikatar ta tunatarwa Trump har yanzun tana jirin randa za’a gabatar da shi a gaban kuliya kan kissahn Janar shahida Qasim Sulaimani, wanda shi gwarzon yaki da kungiyoyin yan ta’adda a Iraqi da Siriya. Shi ya jagoranci kawo karshen mamayar da kungiyoyin Daesh suka yiwa kasashen biyu a shekara 2017.

Ma’aikatar da bayyana Amurka a matsayin kasa wacce ta fi ko wace kasa a duniya goyawa yan ta’adda a yankin Asiya da kudu da kuma wasu wurare, sannan tana amfani da kujerar Veto a kwamitin tsaro na MDD don kare yan ta’adda da kuma hanasu gurfana a gaban kuliya don fuskantar adalci.

Ma’aikatar ta yi watsi da maganar Trump kan cewa shirin Iran na makamashin Nukliya ba ta zaman lafiya bane, ta kuma kara da cewa Trunp bai da wata shaida da take tabbatar da hakan, sannan ta kara da cewa, wannan zargin bai yadda zata halatta kaiwa JMI yaki ba.

Daga karshen ma’aikatar ta tabbatar da cewa kwarar makaman Amurka da na kasashen yamma zuwa HKI shi ne yake jawo rashin zaman lafiya a yankin. Kuma matukar HKI tana nan babu kuma zaman lafiya a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments