Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba za a taba samun katsewa cikin kyakkyawar rawar da Iran ke takawa a gudanar da mu’amalarta ta yanki da ta kasa da kasa ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya jaddada cewa: Ba za a taba samun tsaiko a ci gaba da yunkurin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma rawar da take takawa mai inganci a cikin mu’amalar shiyya-shiyya da kasa da kasa karkashin jagoranci mai hikima da al’ummar Iran mai daraja ba.
A rubutunsa a shafin sada zumunta ya yi magana kan jana’izar shahidi Hujjatul-Islam Ibrahim Ra’isi da shahidi Hossein Amir Abdollahian da sauran shahidai dangane da abin da ya faru na tausayawa na kwanan nan, yana mai jaddada cewa: Iran abar kauna ta yi hasarar shugabanta masoyin al’umma kuma gwaninta mai kwazo, da ministan harkokin wajen kasarta mai fafutuka kuma mai himma, amma a karkashin jagoranci mai hikima da kuma al’ummar Iran mai girma masu tsayiwa a kan duga-dugansu da kuma fadaka, don haka ba za a samu tsagaitawa ba a ci gaban yunkurin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da rawar da take takawa mai inganci a cikin hulɗar yanki da na duniya.