Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana makomar ma’aikatan karamin ofishin jakadancin Iran a birnin Halab na Siriya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi kakkausar suka kan harin da wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda dauke da makamai suka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Halab na kasar Siriya, yana mai jaddada cewa: Karamin ofishin jakadancin Iran da sauran ma’aikatan ofishin jakadancin a birnin Halab suna nan cikin koshin lafiya.
A wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Asabar, Baqa’i ya musanta cewa; An kashe ko jikkata wani daga cikin ma’aikatan karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Halab a shiyar arewacin Siriya, biyo bayan ci gaban da kutsen kungiyoyin ‘yan ta’adda suka yi, yana mai jaddada cewa dukkan ma’aikatan ofishin na cikin koshin lafiya.
Baqa’i ya kara da cewa: Yarjejeniyar 1963 kan huldar ofishin jakadanci ta haramta duk wani abu mai muni ya shafi ofishin jakadanci, kuma duk wani mutum ko kungiya ko gwamnati da ta karya wannan yarjejeniya lamari ne da ba za a amince da shi ba.