Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da kasashen kungiyar G7 saboda shishigin da suke yi a cikin harkokin cikin gida na kasar.
Kamfanin dillancin labaran IRNa na kasar Iran ya nakalto bayanin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran na cewa, wadan nan kasashe karkashin tasirin Amurka sun fito suna maganar abinda suka kira kare hakkin bil’adama a kasar Iran.
Bayanin ya karan da cewa wadan nan kasashe a daddaikunsu suna da matsaloli kare hakkin bil’adama a kansu, banda haka gaba dayansu suna goyon bayan HKI a kissan kiyashin da aika a Gaza, don haka wannan ya isa ya basu da baki a shari’ance kan sanar da wata kashe abinda ake kira kare hakkin bil’adama.
Bayanin ya kara da cewa kungiyar ta G7 ta yi kunnnen uwan shegu da kalaman Trump da kuma HKI na ingiza tashe-tashen hankula a kasar Iran, sun bar wannan saboda munafurci da nuna fuska biyu sun zargin JMI da take abinda suka kira hakkin bil’adama.
Bayanin ya kammala da cewa JMI ba zata taba manda yadda kasashen Jamus, Burtania, Canada da Amurka suka goyi bayan hare-haren da HKI ta kai kan JMI a cikin watan Yunin shekarar da ta gabata ba.