Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Iran Ta Kama Gungun ‘Yan Ta’adda A Lokacin Zaben Kasar

Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Iran ta sanar da kame ‘yan ta’adda tare da dakile makircin kunna wutar tashin hankali a lokacin zaben a kasar

Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Iran ta sanar da kame ‘yan ta’adda tare da dakile makircin kunna wutar tashin hankali a lokacin zaben a kasar

Mataimakin ministan harkokin cikin gidan kasar Iran mai kula da harkokin tsaro da harkokin ‘yan sanda Majeed Mirahmadi ya sanar da kame wasu ‘yan ta’adda tare da dakile wani shiri da makiya suka shirya na bata sunan juyin juya halin Musulunci a lokacin zaben shugaban kasa.

Dangane da batutuwan tsaro da aka tunkara a lokacin zaben shugaban kasar Iran, Mirahmadi ya ce: Kungiyoyin ‘yan ta’adda sun yi shirin haifar da wani yanayi na hargitsa harkokin tsaro a Iran a lokacin zabe ta hanyar aiwatar da ayyukan ta’addanci da kuma haifar da fargaba da tsoro a tsakanin al’ummar kasar don hana su halartar zaben.

Mataimakin ministan harkokin cikin gida na Iran kan harkokin tsaro da ‘yan sanda ya kara da cewa: Wadannan kungiyoyi sun yi kokarin mayar da lokacin zaben zuwa wani babban kalubalen tsaro ta hanyar amfani da dabaru masu tsauri da kuma sanya yanayin rashin tsaro a kasar.

Mirahmadi ya bayyana cewa: Saboda sa ido kan bayanan da manyan jami’an leken asirin Iran suka samu, an kama wasu ‘yan ta’adda da suka shigo Iran kafin zabe, kuma sun samu horon kan nau’o’in ayyukan ta’addancin da suka shirya aiwatarwa a lokacin zaben, amma da taimakon Allah munanan manufofinsu ba su kai ga samu nasara ba.

Mirahmadi ya tabbatar da cewa: Daga cikin makirce-makircen da masu adawa da juyin juya halin Musulunci suka shirya, har da kiraye-kirayen halartar dandalin da suka kebe da sunan magoya bayan daya daga cikin ‘yan takara, ba tare da sanin dan takarar ba, don nuna murnar nasarar da ya samu, wanda aniyarsu ta rushe saboda mutane ba su yi maraba da shi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments