Sama da ma’aikatan Capitol Hill 230 da ba a bayyana sunayensu ba daga ofisoshi 122 sun sanya hannu kan wata wasika da ke kira ga shugabanninsu da su yi zanga-zanga ko kauracewa jawabin da Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda zai yi wa Majalisa a ranar 24 ga Yuli.
Wasikar kungiyar ma’aikatan na Congressional Progressive Staff Association ta kunshi cewa, “Wannan ba batun siyasa ba ne, amma batu ne na ‘yan adamtaka, wanda Jama’a, dalibai, da ‘yan majalisar dokoki a fadin kasar da ma duniya baki daya sun tofa albarkacin bakinsu dangane da matakin da Netanyahu ya dauka a yakin da yake kaddamarwa kan Gaza.”
Wasikar ta yi nuni da karuwar adawa a bangaren masu sassaucin ra’ayi a kan jawabin Netanyahu. ‘Yan majalisar dokokin jam’iyyar Democrat da dama sun sanar da shirin kauracewa jawabin.
‘Yan jam’iyyar Republican sun ba da shawarar gayyatar Netanyahu bayan jawabin da shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Chuck Schumer, babban jami’in Yahudawa a Amurka ya yi, inda ya yi kakkausar suka ga Netanyahu.
A yayin ziyarar tasa, ana sa ran Netanyahu zai gana da Biden, kamar yadda majiyar siyasa ta bayyana, duk da cewa har yanzu Biden bai gayyaci Netanyahu a fadar White House ba.
Wannan dai na zuwa ne yayin da a halin yanzu Netanyahu ke kokarin shawo kan koma bayan da aka samu a cikin gida da waje dangane da manufofinsa kan yakin Gaza, da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da halin da ake ciki a Arewacin falastinu da Isra’ila ta mamaye, da kuma ta’addancin da yahudawa suke yi wa Falasdinawa a yammacin kogin Jordan.