Wanda ya jagoranci sallar juma’a a yau anan birnin Tehran, Hajjatul-Islam Kazim Saddiki, ya bayyana cewa: Trump yana yin baraza da tsoratarwa da cewa zai rage karfin da Iran take da shi a fagen fasahar Nukiliya da kuma matsayin da take da shi a cikin wannan yankin na yammacin Asiya, sai dai kuma ya kamata ya fahimci cewa kamar yadda shugaban da ya gabace shi ya yi kuskuren lissafi, to shi ma haka yake yi.”
Limamin na Tehran ya kuma ce,Kamar yadda shugaban Amurka da ya gabaci Trump bai sami nasara akan Iran ba, shi ma haka ba zai cimma manufarsa ba.
Hajjtul-Islam Siddiki ya kuma kara da cewa; Bai kamata ace muna kallon cewa ta hanyar abubuwa na zahiri ne kadai za a iya warware matsaloli ba,domin wannan shi ne koyawar tauhidi a cikin alkur’ani mai girma. Haka nan kuma ya yi kira da kar a biye da mika kai ga sha’awace-sha’awace na duniya ba, maimakon haka mu mika kai da yin biyayya ga dokokin Allah domin mu sami haskakawa akan hanyar da muke tafiya a kanta.
Da yake magana akan kwanaki 10 na cin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran, Limamin na Tehran ta ce, abinda ya faru yana cike da darussa da al’umma za ta dauki darussa daga ciki har adaba. Kuma gagarumin sauyin da ya faru a cikin al’ummar Iran yana daga cikin manufar da juyi ya cimmawa a karkashin jagorancin Imam Khumaini (r.a).
Haka nan kuma ya bayyana cewa;siffa mafi girma da take tattare da juyin shi ne kasantuwarsa ta musulunci, kuma a lokaci daya akan tsarin jamhuriya.