Limamin Tehran: Amurka Tana Son Bude Tataunawa Da Iran Ne Domin Fada Da Juyin Juya Hali

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran Ayatullah Ahamd Khatami  ya ce; Wajibi ne duniya ta san cewa, matsayar Iran dangane da Amurka shi ne

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran Ayatullah Ahamd Khatami  ya ce; Wajibi ne duniya ta san cewa, matsayar Iran dangane da Amurka shi ne wanda Imam Khumaini da kuma jagoran juyin musulunci suke bayyanawa wanda ya dauki Amurka a matsayin; Babbar shaidaniya.”

Ayatullah Khamati ya kuma kara da cewa; A lokuta da dama jagoran juyin musulunci  ya sha nanata wannan zance, a dalilin haka muna yin kira ga  banagren da za a yi tattaunawar da su, da su fahimci cewa manufar Amruka shi ne kalubalantar juyin juya hali.

Dangane da karatowar ranar Saukar Wahayi ga manzon Allah ( s.aw.) limamin na Tehran ya ce, ranar aiko manzon Allah, ( s.a.w) rana ce, mai girma ga jinsin bil’adama, wacce ake daukar ta ta murna da  yin bukukuwa a Iran.

Ayatullah Khatami ya kuma ambaci karatowar ranakun cin nasarar juyin musulunci, da cikarsa shekaru 46, yana mai bayyana su a matsayin ranakun Allah.

Haka nan kuma ya yi fatan ganin al’ummar Iran sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin shiga cikin jerin gwanon da aka saba yi a kowace shekara a wannan ranar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments