A sabbin hare haren da jiragen yakin HKI suka kai kan kasar Lebanon, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, majiyar ma’aikatar lafiya ta kasar ta bayyana cewa wannan shi ne hare hare mafi muni tun bayan fara yaki a kan kasar Lebanon.
Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon na fadar haka, ta kuma kara da cewa mutane akalla 88 ne suka yi sahada a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a kuma yankuna daban daban na kasar. Banda haka wasu mutane 153 sun ji rauni.
Labarin ya kara da cewa jiragen yakin HKI sun kai hare hare masu yawa a yankuna daban daban wadanda suka hada da yankunan Biqa, Jabal Lebanon da sauransu.
Jiragen saman yakin yahudawan sun kai hare hare kan birnin Ba’alabak, Saida, Marja’iyyun, Bintijbail, Jizzeen da sauransu.