Wasu lauyoyi 77 a Jamus sun bukaci gwamnatin kasar da ta mutunta sammacin kotun hukunta manya laifuka ta duniya ICC, na cafke firaministan Isra’ila Banjamin Netanyahu.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da da suka fitar, fitattun lauyoyin 77 sun kuma bayyana yiwuwar kasancewar Netanyahu a Jamus a matsayin take doka da kuma hakkin kasar.
Lauyoyin sun soki Friedrich Martin Josef Merz, dan siyasa kuma shugaban gwamnati a nan gaba, saboda sanarwar da ya yi a lokacin yakin neman zabe cewa zai samo hanyar gayyatar firaministan Isra’ila da kuma tattaunawa ta wayar tarho da Netanyahu bayan nasararsa.
Lauyoyin sun kuma yi Allah wadai da halin wasu jami’o’in da suka soke jawabin da Francesca Albanese mai kula da harkokin kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi a yankin Falasdinu.