Larijani: Muna Tare Da Duk Matakin Da Gwamnati Da Al’ummar Lebanon Su Ka Dauka

Dr. Ali Larijani ya isa birnin Beirut  na kasar Lebanon inda ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar da su ka hada Fira minista na

Dr. Ali Larijani ya isa birnin Beirut  na kasar Lebanon inda ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar da su ka hada Fira minista na riko Najib Mikati, da shugaban majalisar dokoki Nabih Barri, domin isar da sako na musamman daga jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei.

Dr. Ali Larijani  wanda ya gabatar da taron manema labaru  ya bayyana cewa; Duk wani mataki da kungiyar gwgawarmaya da kuma gwamnatin Lebanon za su dauka, mun amince da shi,kuma muna goyon bayansu.

Har ila yau Dr. Larijani ya ce; Muna tare da gwamnati da kuma al’ummar Lebanon a cikin kowane yanayi, muna kuma yin kira ga gwamnati da ta tantance a tsakanin abokai da makiya.

Dr. Ali Larijani ya kuma ce; Na yi tattaunawa da kuma shawara da jami’an gwamnatin Lebanon akan hanyoyin warware matsalolin da ake fuskanta da su ka shafi rayuwar al’ummar Lebanon.”

Dr. Ali Larijani ya kara da cewa; shugaban Majalisar dokokin ta Lebanon ya yi cikakken bayani mai kyau akan halin da ake ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments