Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara Dr. Ali Larijani ya ce, idan har Amurka da Isra’ila su ka fake da batun shirin makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, su ka kawo mata hari, to ya zama wajibi a gare ta ta kera makaman Nukiliya.
Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din Iran ta yi jira da shi a jiya Litinin da dare, ya bayyana cewa; manyan kasashen duniya suna son yin alaka kai tsare da Iran cikin ‘yanci, sai dai suna da fuskantar matsin lamba daga Amurka.
Tsohon shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran ya kuma kara da cewa; Idan har Amruka da HKI su ka kawo wa Iran hari, to, za ta dau hanyar kera makaman Nukiliya, kuma su kansu al’ummar kasa abinda za su so ganin ya faru kenan.
Dr. Ali Larijani wanda memba ne a cikin majalisar fayyace maslahar tsaron musulunci, ya kara da cewa; Yaki da Iran ba abu ne mai sauki ba, yana da tattare da hatsarin da zai koma kan mahara.
Larijani ya kuma ce; Fatawar Jagora ita ce, ta haramta mallakar makamin Nukiliya,amma idan Amurka ta yi kuskure, to matsin lambar mutane zai sa Iran ta kama hanyar kera makaman Nukiliya.
Har ila yau, Larijani ya ce; Fasahar Nukiliya da Iran take da ita, an tsara ta akan cewa, ko da an kawo wa Iran din hare-hare, to za ta ci gaba da aiki ba tare da tsaiko ba. Kum su kansu masu hankali daga cikin makiya sun san cewa idan su ka kawo wa Iran farmaki, to kuwa za ta daura damarar kera makaman Nukiliya.